Jami’an yan sanda a Abuja sun tarwatsa masu zanga-zanga da su ka fito yau Litinin.

An tarwatsa masu zanga-zangar ne a Maitama ta hanyar harba hayaki mai sa hawaye.

Masu zanga-zangarsun fito yau don jan hankalin gwamnati ma ganin ta dauki matakin gaggawa kan tsadar rayuwa da tattalin arziki da kuma nuna rashin amincewa da dokar laifuka ta yanar gizo.

Zanga-zangar dai ana yinta a yau wadda aka kira ta ta kasa kuma ƙungiyar Take It Back da goyon bayan wasu kungiyoyin fararen hula su ka shirya.

Tun a jiya Lahadi ƴan sanda a Najeriya su ka bukaci masu zanga-zangar da su janye.

Mai sanya idanu kan shirya zanga-zangar da kungiyar Take It Back su ka shirya Juwon Sanyaolu ya ce sun shirya zanga-zangar ne bisa rashin tsaro a kasa da hauhawar farashin kayayyaki da kuma sanya dokar ta baci da aka yi a jihar Rivers.

A yau dai ake tunanin manyan jami’an yan sanda za su halarci babban taro da za su yi a matsayin ranar yan sanda ta duniya wanda ya sanya aka rufe wasu manyan hanyoyin a Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: