Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta musanta rade-raden cewa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sauke shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakub daga shugabancin hukumar.

Bayan bullar jita-jitar da ake yadawa a shafukan sada zumunta, hukumar ta musanta batun ta na mai cewa shugabanta Mahmud Yakub na nan akan mukaminsa.
A sakon da ake yadawa na nuni da cewa shugaban Kasa Bola Tinubu ya sauke Farfesa Yakubu daga shugabancin hukumar, inda ya nada Farfesa Bashiru Olamilekan a matsayin shugaban hukumar ta INEC.

A wata tattaunawa da mai magana da yawun ofishin shugaban hukumar Rotimi Oyekanmi ya yi da jaridar Vanguard ya bayyana cewa babu gaskiya a cikin wallafar da ake yadawa, yana mai neman mutane su yi watsi da ita.
