Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Kasa NCDC ta ce mutane 151 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar shankarau a Kasar.

A cikin wata wallafa da Hukumra ta fitar a jiya Lahadi ta ce daga cikin Jihohin da mutane suka fi mutuwa sun hada da Sokoto, Kebbi, Kano, Jigawa, Katsina, Adamawa, Bauchi, Gombe, Borno, Yobe, da kuma Oyo.

Sannan NCDC ta ce Jihohin Katsina, Jigawa, Adamawa, Yobe, Gombe, Kebbi da Sokoto su ne Jihohin da ke akan gaba a masu dauke cutar.

Hukumar ta kuma tabbatar da kamuwar mutane 126 daga cikin mutane 1,858 da ake kyautata zaton na dauke da cutar a wasu daga cikin Jihohin.

A cikin alkaluman da hukumar ta fitar kan cutar ta bayyana cewa adadin mutane 74 da suka kamu da cutar ya kai 156 a wasu Jihohin 23 na fadin Kasar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: