Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta rade-raden da ke yawo cewa jami’an soji Kasar nan sun hana Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima shiga Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Musantawar na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da hadimin shugaban Kasa yada labarai a Ofishin Mataimakin shugaban Kasa Stanley Nkwocha ya fitar a yau Asabar.
Sanarwar ta bayyana cewa babu wani lokacin da bai’wa jami’an tsaro izinin rufe hanya domin hana Shettima shiga fadar shugaban kasa.

Acewar Sanatar akwai kyakkyawar fahimta kyau tsakanin shugaban Tinubu da Shettima, kuma dukkan wani kokari na tada zaune a tsakanin su hakan ba zai yi tasiri ba.

Sanarwar ta ce masu yada irin wadandan rahotanni marasa gaskiya a cikinsu su na yi ne domin da nufin haddasa rikici a tsakanin shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakin nasa.
Acewar Sanarwar ana rada irin wadandan rahotanni ne daga shafukan bogi, kuma manufarsu shine ta tayar da hankula da kuma jefa fadar shugaban kasa cikin rikici.
Hadimin ya kara da cewa gwamnatin ta tarayya na da himmar ci gaba da gudanar da mulkinta cikin gaskiya da hadin kai.
Sanarwar ta bayyana cewa babu kanshin gaskiya a cikin jita-jitar da ake yadawa, inda ta bukaci mutane da su yi watsi da ita, tare da yin kira ga ‘yan Kasar nan da su ci gaba da goyon bayan Shugaba Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima da kuma kaucewa labarin da babu gaskiya a cikinsa.
Rahotannin da ake yada na nuni da cewa sojojin sun tare ƙofar shiga fadar shugaban ƙasa da cewa umarni ne daga sama ya koma gidansa da ke makwabtaka da fadar shugaban kasa, zuwa lokacin da Shugaba Tinubu ya dawo daga ziyarar aiki da ya kai ƙasar Faransa.