Tsohon hadimin shugaban ƙasa kan harkokin siyasa Hakeem Baba Ahmed ya ce nan da watanni shida masu zuwa arewa za ta tsayar da ɗan takarar da za ta marawa baya.

Baba Ahmed ya kuma ce babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa da zai lashe zaɓe a Najeriya ba tare da samun goyon bayan ƴan arewacin kasar ba.

Hakeem Baba Ahmed dai shine mai magana da yawun ƙungiyar dattawan arewa, sai dai ya samu mukami a gwamnatin shugaba Bola Tinubu wanda a kwanakin baya ya ajiye.

A wani faifan bidiyo da ya karade kafofin sa da zumunta a yau, an hango Baba Ahmed a ciki na jawabi yayin da a gefe guda akahango Farfesa Usman Yusuf tsohon sakatare a hukumar inshorar lafiya ta Najeriya.

A cewar Baba Ahmed a yanzu yan arewa sun waye bayan ɗaukar lokaci da su ka shafe su na shan wahala.

Ya ce arewa na buƙatar gwamnatin fa za ta fahimci matsalolinsu da kuma magancesu

Wannan dai na zuwa ne yayin da ake ta shirin tunkarar babban zaben shekarar 2027 da ke tafe

Leave a Reply

%d bloggers like this: