Mataimakin shugaban Najeriya Sanata Kashin Shettima ya musanta zargin hanashi shiga fadar shugaban ƙasa.

Shettima ya musanta hakan da kansa ta bakin babban hadiminsa kan yaɗa labarai Mista Stanley Nkwocha, ya ce batun da ake yaɗa sam bashi da tushe balle makama.

Wata jaridar yanar gizo ce ta wallafa ranar Juma’a cewar, jami’an tsaro sun hana mataimakin shugaban ƙasar shiga fadar shugaban ƙasa.

Sai dai sanarwar ta ce sam batun ba haka yake ba.

Sanarwar ta ce makamancin haka ba ta taɓa faruwa ba.

Idan za a iya tunawa fadar shugaban ƙasa ma ta musanta batun wanda ta ce an ƙirƙiri hakan ne domin kawo ruɗani a tsakanin mutane.

Leave a Reply

%d bloggers like this: