Gwamnan Jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya ya mika sakon jaje bisa mutuwar mutane Biyar, tare da jikkatar wasu Takwas bayan wata mota ta afka musu a jihar a yau Litinin.

Mai magana da yawun gwamnan Isma’il Uba Missali ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau.

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan ya kadu matuka bayan samun rahoton faruwar lamarin, yana mai cewa lamarin yana da taba zuciya.

Misalli ya kara da cewa gwamnantin Jihar za kuma ta dauki nauyin maganin wadanda suka jikkata.

Acewarsa gwamnatin Jihar ta Gombe, za ta tabbatar da ganin ta dauki matakan kare afkuwar irin hakan anan gaba.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: