Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Ƙasa NDLEA ta tabbatar da kama wani mutum mai suna Ayuba Ashiru mai shekaru 80 a duniya, dauke da kilogiram 2.3 na miyagun kwayoyi a tare dashi.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ya fitar a yau Lahadi.

Babafemi ya bayyana cewa jami’ansu sun kama Asiru ne a ranar 14 ga watan Mayun da muke ciki a yankin Dogarawa da ke cikin ƙaramar hukumar Sabon Garin a Jihar Kaduna ne bayan sun samu bayanan sirri akansa.

Kakakin ya kara da cewa a baya ma an taɓa kama Ayuba Ashiru dauke da miyagun kwayoyi, inda aka aike dashi gidan ajiya da gyaran hali na tsawon shekaru Goma tsakanin 2014 zuwa 2024.

Femi ya ce wanda ake zargin ya kasance cikin safarar miyagun kwayoyi tsawon shekaru 46.

A wani bangaren kuma hukumar ta bayyana cewa jami’anta sun kama wata tsohuwa mai shekaru 82 mai suna Uloma Uchechi Sunday, tare da Ɗiyarta mai shekara 32 mai suna Chisom Uchechi a jihar Abia dauke suma da miyagun ƙwayoyi.

Hukumar ta bayyana cewa ta kama matar da ƴarta ta ne a jiya Asabar 17 ga watan nan na Mayu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: