Gwamnatin tarayya ta amince bayyana cewa wasu ofisoshin diflomasiyya da ofishin jakadancin Najeriya a kasashen waje na fuskantar kalubale na kudade da na ayyuka, tun daga rashin biyan albashin ma’aikata zuwa yawan basussukan da ake bin masu gidaje da masu hidima.

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai dauke da sanya hannun mai magana da yawunta Mista Kimiebi Ebienfa da ta fitar a ranar Litinin.
Ta ce matsalolin sun kawo cikas ga tafiyar da ofisoshin jakadanci, harma da karamin ofishin jakadancin Kasar a kasashe daban-daban.

Ma’aikatar ta danganta matsalar rashin kudi a halin yanzu da yanayin tattalin arzikin cikin gida na Najeriya, inda ta ce ayyukan ba su tsira daga kalubalen da cibiyoyin gwamnati ke fuskanta a cikin gida ba.

Sanarwar ta bayar da tabbacin cewa jin dadin ma’aikata a kasashen waje ya kasance babban fifikon gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu, tana mai jaddada cewa tuni an fara aiwatar da matakan magance matsalar.
Acewarta gwamnati na daukar kwararan matakai masu inganci don tunkarar abubuwan da suka shafi rabon kudade ga dukkan Ma’aikatunta na kasashen waje, inda ta ce daya daga cikin irin matakin shine amincewa da kuma fitar da kuɗaɗen na musamman don rage wahalhalun da wasu Ma’aikatu ke fuskanta.
Akarshe ta ce ma’aikatar ta kafa wani kwamiti na musamman da zai tabbatar da bayanan basussukan da ake bin su domin tabbatar da ganin an kammala biya.
