Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a 5 ga Satumban 2025 a matsayin ranar hutu domin tunawa da ranar da aka haifi Annabi Muhammad S,A,W.

Ministan harkokin cikin gida Dr Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya a wata sanarwa da babban sakatariyar ma’aikatar, Dr Magdalene Ajani ta fitar a ranar Talata.
Tunji ya kuma taya al’ummar Musulmin Najeriya da sauran kasashen duniya murna ranar, inda ya bukaci yin tunani a kan kyawawan dabi’un Manzon Allah S,A,W na zaman lafiya, soyayya, tawali’u, juriya, da kuma tausayi.

Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya na dukkan addinai da su yi amfani da wannan damar wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a kasar, tare da marawa yunkurin gwamnati baya na hadin kai da ci gaban Kasa.

Sanarwar ta kara da cewa, Ministan harkokin cikin gida na yi wa daukacin musulmi musulmi murnar zagayowar ranar.
