Rundunar ‘yan sandan Jihar Anambra da ke aiki a ofishin ‘yan sanda na Awada da ke karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar ta ceto wani matashi mai shekaru 28 da yayi yunkurin hallaka kan shi.

Jami in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar SP Tochukwu Ikenga ya ce matashin mai suna Mr Okudili David Onyiba an ceto shi ne ranar Talatar da ta gabata, bayan hawan babban layin wutar lantarki da nufin hallaka kansa.

Ikenga ya bayyana cewa bayan samun rahoton faruwar lamarin daga mazauna yankin, jami’an suka garzaya gurin da ke kan titin NEPA da ke Awada in da matashin ya ke yunkurin hawa kan kayan wutar lantarkin.

Kakakin ya ce ‘yan sanda da masu bayar da taimakon gaggawa sun dauki tsawon lokaci kafin su ceto matashin.

Ikenga ya kara da cewa sun dauki matashi, tare da tafiya da shi ofishin ‘yan sandan, domin duba lafiyar da kuma yi masa gwajin kwakwalwa.

Kwamishinan yan sandan jihar CP Ikioye Orutugu ya shawarci duk wadanda ke fuskantan matsin rayuwa a jihar da su bayyana wa yan uwa, abokai da cibiyoyin da abin ya shafa maimakon yunkurin hallaka kansu.

Yan sandan sun kuma ja hankalin al umma da su magance matsalolin kansu ta hanyar tattaunawa da yan’ uwa, abokai, tare da neman taimako daga kungiyoyi daban daban.

Leave a Reply

%d bloggers like this: