Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da ranakun komawa makarantu a Fadin Jihar, bayan karewar hutun karshen zago da aka bayar.

A cewar wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi Balarabe Abdullahi Kiru ya sanya wa hannu, ta ce za a koma makarantun kwana a ranar Lahadi 7 ga Satumba, yayin da za a koma makarantun da bana kwana ba a ranar Litinin 8 ga Satumba.
Sanarwar ta yi kira ga iyaye da masu kula da su kula da ranakun da za a koma makarantun, inda ta yi gargadin cewa dalibai da suka gaza za wajen komawa makarantun za su fuskanci hukuncin ladabtarwa.

Kwamishinan ma’aikatar Dr Ali Haruna Makoda ya yiwa malamai da dalibai fatan samun nasarar a cikin karatunsu.

Kwamishinan ya sa ke jaddada aniyar ma’aikatar na gudanar da ayyukan sanya ido akai-akai don tabbatar da ingancin ma’aikata da zuwansu makaranta a kan lokaci.
