Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya ce ‘yan bindiga za su zama tarihi a jiharsa idan har ya mallaki jami’an tsaro a kasar.

Gwamna Lawal ya ce yana sa ne da motsin duk wani dan bindiga da ke aiki a jihar, inda ya ce babban abin da ke damun sa a yakin da ake yi da ‘yan bindiga shi ne rashin kula da hukumomin tsaro kai tsaye.
Ya kuma jaddada cewa shugabannin tsaro a Jihar na karbar umarni ne kawai daga Abuja, inda ya koka da cewa suna da wurare da dama na bin diddigin wadanda suka gyara a fadin jihar don kawai a taimaka wa tsaro wajen gano ‘yan bindigar.

Gwamnan yayi rantsuwa da Allah da cewa, duk inda shugaban ‘yan bindiga ya ke a cikin jihar Zamfara, ya san shi kuma dukkan inda ya fita ya sani.

Dauda ya kara da cewa da wayar hannu zai iya nuna, inda wadannan ‘yan bindiga suke, sai dai ya ce ba za su iya yin wani abu da ya wuce ikonsu ba.
Acewarsa idan yana da ikon bayar da umarni ga jami’an tsaro, yana mai tabbatar da cewa, za su kawo karshen ‘yan ta’addan a jihar nan da watanni biyu.
Gwamnan ya ce sau da yawan lokuta yana zubar da hawaye ga mutanensa saboda yana iya ganin matsala amma saboda ba shi da iko a kan hukumomin tsaro, ba zai iya bayar da umarnin ga jami’an tsaro ba kan su dauki mataki a kan lokaci.
Gwamnan ya kum koka akan sauran wasu abubuwa da suka shafi Jihar, sai dai ya ce suna iya bakin kokarinsu wajen ganin matsalar ta zama tarihi a Jihar.
