Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fitar da wasu sabbin guraben aikin gona, wanda ta ce za ta iya samar da ayyukan yi miliyan 21 a kasar.

Har ila yau, ta yi alkawarin yin garambawul don fadada noman, inganta samar da lamuni da samar da miliyoyin ayyukan yi a yankunan karkara karkashin shirin tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu.

Mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima ne ya bayyana tsare-tsaren ga kungiyar Abinci da Aikin Noma ta kasa da kuma na kasa da kasa da zuba jari a Abuja.

Shettima ya bayyana yunwa a matsayin babbar illar da ke bayyana raunin gwamnati, da kuma raunin da ake samu.

Babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa, Stanley Nkwocha, ne ya bayyana cikakken bayanin taron na ranar Talata a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Ƙarin ƙarfafa manoma yayin da gwamnatin tarayya ta buɗe sabbin hanyoyin saka hannun jari bangaren na noma.

Matakan sun hada da samar da dandalin yanar gizo, ƙarfafa tsarin bashi na aikin gona, manyan injiniyoyi, da dabarun ban ruwa.

Shettima ya ce Najeriya na da karfin ban ruwa fiye da hekta miliyan uku na gonaki amma a halin yanzu tana amfani da kasa da kashi 10 cikin 100 na wannan damar.

Yace saka hannun jari mai mahimmanci a cikin ban ruwa kadai zai iya ninka amfanin gona sau uku, ya ‘yantar da Kasar daga dogaro na yanayi, da kuma karfafa juriya kan sauyin yanayi.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa tsarin Najeriya na shirin bunkasa kasa na shekarar 2021-2025 na da nufin fitar da mutane miliyan 35 daga kangin talauci, samar da ayyukan yi miliyan 21 a yankunan karkara da samar da isasshen abinci da abinci mai gina jiki.

Shettima ya yi nuni da cewa noman rani na kawo sauyi, inda ya ce Najeriya na da magudanan ruwa da za su iya noman sama da hekta miliyan uku amma a halin yanzu ana amfani da kasa da kashi goma cikin dari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: