Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wani sojan bogi da wasu mutane uku da ake zargin barayin mota ne bayan wani hatsarin mota da ya rutsa da su.

A wata sanarwa da Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Lawan Shi’isu Adam ya fitar a ranar Laraba a garin Dutse babban birnin jihar, ya ce lamarin ya faru ne a ranar 8 ga watan Satumban nan da misalin karfe 7:50 na safe a kauyen Sabon Sara da ke karamar hukumar Kafin Hausa.

Sanarwar ta ce jami’an ‘yan sanda na Kafin Hausa ne suka kama wadanda ake zargin bayan sun gudu daga inda hadarin ya faru.

Wadanda ake zargin dukkansu ‘yan asalin jihar Kano ne, Kabiru Musa mai shekaru 35 a unguwar Rimin Kebe, da Umar Ali mai shekaru 25, na Haye, da Sabiu Bashir mai shekaru 25 a kauyen Tokarawa.

Acewar sanarwar kafin kama su, jami’an sun samu rahoto a ranar 7 ga watan Satumba game da satar wata mota, daga tashar mota ta Agura, a karamar hukumar Kafin Hausa.

A binciken farko ya nuna cewa Kabiru Musa ya yi ikirarin cewa yana aiki da rundunar soji ta 102 da ke Abuja, tare da gano cewa ba wannan ne karon farko ba da ya ke aikata laifuka.

Karin binciken da hukumar binciken manyan laifuka ta jiha da ke Dutse ta yi ta tabbatar da cewa shi mai aikata laifuka ne.

Sannaan a binciken da aka yi a kayayyakin Kabiru an gano katin cirar kudi na ATM guda bakwai, lasisin tuki guda biyu, da wasu abubuwa da ke da alaka da ayyukan damfara.

Dukkan wadanda ake zargi yanzu haka suna fuskantar tuhuma a kotu bayan kammala bincike.

Sanarwar ta bukaci al’ummar Jihar da su sanya ido, tare da gaggauta kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa kan ayyukan batagari.

Kwamishinan ‘yan sandan, CP Dahiru Muhammad, ya yabawa jami’an na Kafin Hausa, bisa daukar matakin da suka yi na kama wadanda ake zargi.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: