Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani, ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa ba za ta ciyo bashi ba, don gudanar da ayyuka ko kuma tara basussuka yayin aiwatar da su.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da ginin titi mai tsawon kilomita 16.5 wanda ya hada garuruwan Kayarda Tasha, Kayarda Gari, Unguwan Sarki, Maskawa, da Dan Alhaji a karamar hukumar Lere.
A yayin kaddamarwar gwamnan ya tabbatar wa mazauna yankin cewa za a kammala ayyukan da aka yi watsi da su kafin karshen wa’adin mulkinsa.

Gwamna ya bayyana cewa aikin titin da ya kaddamar zai gudana ne daga wani kamfani, inda ya ce irin wannan aikin ba a taba yin irinsa ba a karamar hukumar Lere.

Da ya ke bayyana wasu ayyukan da gwamnatinsa ta gada ya ce, an kammala gadar Rewa da ta hada garin Gure, haka nan an kammala gadar Marjeri, inda za su kammala gadar Tudai nan da wata daya ko biyu masu zuwa.
Gwamna Sani ya ce ya dauki matakin magance matsalar karancin wutar lantarki a garuruwan Yarkasuwa, Kayarda, Ramin Kura da kuma Mariri duk a Jihar.
A jawabin Kwamishinan Muhalli na Jihar Alhaji Abubakar Buba, ya yabawa kokarin gwamnan na cika alkawuran da ya dauka, inda ya bayyana gwamnan a matsayin mutum mai cika alkawari.
Ya kuma yaba wa gwamnan bisa yadda ya bai’wa jami’an gwamnatinsa damar gudanar da ayyukansu cikin walwala.