Kwamitin majalisar dattawa mai kula da kananan hukumomin babban birnin tarayya Abuja ya yi kira ga mambobin kungiyar likitoci ta kasa reshen babban birnin tarayya Abuja, da su gaggauta dakatar da yajin aikin da suke yi.

Kwamitin ya kuma yi alkawarin yin gaggawar ganawa da ministan babban birnin tarayya Nyesom Wike, domin magance bukatun likitocin tare da samun matsaya.
A wani taron gaggawa da aka gudanar a yau Alhamis, kwamitin karkashin jagorancin shugaban kungiyar Sanata David Jimkuta daga Taraba ta Kudu, ya gana da shugabannin lkungiyar da suka shiga yajin aikin.

Kwamitin ya bayar da tabbacin cewa damuwarsu na samun kulawa, kuma sun yi alkawarin za su kara kai tsaye ga Ministan babban birnin tarayya.

Sanata Jimkuta ya amince da mummunan tasirin da yajin aikin ke yi a fannin kiwon lafiya a yankin, sannan ya roki likitocin da su koma bakin aiki yayin da su ke ci gaba da tattaunawa.
Ya yaba wa likitocin kan abin da ya bayyana a matsayin yaki da rashin son kai, inda ya ce bukatarsu ta mayar da hankali ne wajen karfafa tsarin kiwon lafiya da ke durkushewa a Najeriya maimakon biyan bukatun kansu.