Gwamnatin jihar Nasarawa ta yi gargadi ga masu kula da mayankar dabbobi da ke karamar hukumar Akwanga a jihar, tare da yin barazanar rufeta matukar ba a inganta yanayin tsaftar muhalli na wata guda ba.

Kwamishiniyar Muhalli da Albarkatun kasa, Margaret Elayo ce ta yi wannan gargadin a yau Asabar, yayin da take zantawa da manema labarai jim kadan bayan gudanar da aikin tsaftar muhalli a Akwanga na watan Satumban nan.
Kwamishinar wadda ta samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar, Hussaini Babayayi, ya bayyana cewa rashin tsaftar mahautar, na haifar da babbar barazana ga lafiya da jindadin mazauna wurin.

Ta bayyana cewa, tawagar ma’aikatar sun duba wurin a lokacin aikin tsaftar mahalli na wata-wata, inda suka gano rashin kyawun da mahautar ke da shu.

Elayo ta jaddada bukatar bin ka’idojin tsaftar muhalli, tana mai tabbatar da cewa ma’aikatar za ta sanya ido sosai kan ayyukan mahautar tun daga yanzu har zuwa karshen watan Oktoba, domin tabbatar da tsafta da bin ka’idojin tsaftar muhalli na jihar.
