Kungiyar malaman jinya da ungozoma ta kasa reshen jihar Zamfara, ta fara yajin aikin gargadi na kwanaki shida a fadin manyan asibitoci mallakar jihar.

Shugaban kungiyar Kwamared Sani Shehu, ya ce sun dauki matakin ne, domin jawo hankalin gwamnatin jihar, kan korafe-korafen su game da sabon tsarin albashi.

Ya bayyana cewa yayin da gwamnatin jihar ta amince da sabon tsarin albashi na Consolidated Medical Salary Structure a watan Yuni, inda ta yi watsi da tsarin albashi na CONHESS.

Shehu ya bayyana cewa kafin daukar matakin, sai da kungiyar ta, ta nemi ji daga gwamnati har zuwa watan Agusta, sai dai babu wani sakamako mai kyau daga bangaren gwamnati.

Hakan na zuwa ne bayan da kungiyar ta tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai a ranar 11 ga watan Satumba, wanda aka dakatar da shi sa’o’i 24 bayan shiga tsakani da gwamnati ta yi.

Sai dai shugaban kungiyar ya ce yanzu haka sun koma yajin aikin da suka dakatar, inda mambobin kungiyar za su ci gaba da yajin aikin na kwanaki shida daga yau Asabar zuwa Talata mai zuwa.

Acewarsa idan har bayan kwanaki shida ba a biya musu bukatunsu ba, kungiyar za ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: