Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya NRC ta bayyana cewa titin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna zai koma aiki a mako mai zuwa.

Hakan ya biyo bayan nasarar kammala gyare-gyare da tabbatar da tsaro a yankin da abin ya shafa.
Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Asabar, sai dai ba ta bayyana ranar da jirgin zai dawo aiki a hanyar ba.

Idan baku manta ba dakatar da aikin jirgin ya biyo bayan wani jirgi da ya kauce hanya a ranar 26 ga Agustan da ta gabata a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta Abuja zuwa Kaduna.

Babban jami’in hulda da jama’a na hukumar Callistus Unyimadu, ya ce kamfanin ya yi aiki tukuru don tabbatar da cewa ba a kara samun wata matsala ba.
Ya ce a wani bangare na kudurin hukumar na kyautata jin dadin fasinjoji, hukumar NRC ta mayarwa fasinjoji 512 kudadensu daga cikin 583 da ke cikin jirgin da abin ya shafa, inda ya ce ana ci gaba da kokarin kai’wa sauran fasinjojin kudadensu don ganin cewa ba a bar kowa a baya ba.
Kazalika ya kara da cewa hukumar ta kuma yaba da gagarumin goyon bayan da Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya, da hukumomin tsaro, da ‘yan jarida, da masu ruwa da tsaki suka bayar a lokacin da abin ya faru.
