Ministan babban birnin tarayya Nysome Wike ya mayar da babban birnin tarayya a matsayin gurin da yafi kwanciyar hankali a cikin Najeriya ta bangaren tsaro tare da magance rashin tsaro.

A sakon shi na taya kasa murnar zagayowar shekarar samun yanci ga al ummar babban birnin tarayyar a yau laraba ya nuna farin cikin sa na hadin kan yan kasa tare da bayyana abubuwan da ya cimma hadi da abubuwan da shugaban kasa Bola Ahmad tinubu yake son cimma ƙarƙashin tsarin nan na sabunta fata.
Ya kuma yi kira ga al ummar yanki da su ci gaba da karfafawa juna gwiwa tare da tabbatar da cewa basu kauce kan hanyar da iyayen kasa suka dora su ba.

Ministan ya nuna godiyarsa ga irin goyon bayan da al ummar yankin su ka nuna wajen taya shugaba tinubu cimma burin sa kan bunkasa tattalin arzikin kasa, samar da tsaro, tsaron abinci, tabbataccen cigaba da kuma bunkasa ma’aikatu.

Ya ce da goyon bayan gwamnatin tarayya zasu cigaba da samar da manyan ma aikatu da ababen more rayuwa ga al’ umma tare da samar da tituna.
Ya ƙara da cewa kamar yadda aka sani babu garin da zai cika gari ba tareda samun hanyoyin masu kyau ba shiyasa su ka mayar da hankali wajen samar da ingantattun tituna.
Ya kuma ce sun gyara makarantu da asibitoci da dama tare da samar da kayyayyakin aiki da ma aikata.
Ministan ya kuma kara bayyana gabatowar zaben kananan hukumomi wanda za ayi a 26 ga watan fabrairun shekarar 2026 wanda shirye-shirye su ka kankama wajen shirin da hukumar zaɓe ke yi.
Yayi kira ga al ummar yankin da su fita su zabi wanda su ke so cikin kwanciyar hankali da lumana, don tallata shugabannin da su ke da manufa mai kyau da kuma aniyar samar da cigaban kasa ga al umma.
Ya kuma yi kira ga al ummar yankin da su hada gwiwa da jami an tsaro domin samar da tsaro, tabbatar da doka da oda a ko da yaushe tare da jaddawa al’ummar da su zama masu sa ido da kuma sanarwa da jami’an tsaro duk wani motsin da basu gamsu da shi ba.