Ƙungiyar kiristoci ta Najeriya CAN ta bayyana cewa miliyoyin ƴan ƙasa na cikin matsi, yunwa, rashin tsaro, rashin aikin yi, duk da ƙoƙarin sake ginata, tare da cewa samun ainahin cigaban ƙididdigar tattalin arziki na bayyana cikin faɗin kasar.

Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Archbishop Daniel Okoh ya fitar yayin jawabin taya Najeriya murnar cika shekaru 65, ya kuma bukaci shuwagabanni da su samar da abinci, tsaro, kare rayukan al’umma da samarwa da matasa ayyukan yi.

Ya kuma kara da cewa tabbataccan haɗin kai shine jigon cigaban kowacce al’umma tare da samar da wadataccan abinci, da kuma tsaro a kowanne yanki.

Sun kuma yadda Najeriya na da mashahurin kundin cigaba ta bangaran ilimi, lafiya, masana’antu, noma da ma bangaran sadarwa tun kafin samun yancin kai.

Kazalika kuma ya yi addu’a ga shuwagabannin ƙasar da su ƙara himmar karfafa gwiwa wajen ganin an sake gina sabuwar Najeriya mai cike da tsaro.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci jam’ian tsaro da su haɗa kai da al’umma wajen ganin an samu tabbatar da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa.Ƙungiyar kiristoci ta Najeriya CAN ta bayyana cewa miliyoyin ƴan ƙasa na cikin matsi, yunwa, rashin tsaro, rashin aikin yi, duk da ƙoƙarin sake ginata, tare da cewa samun ainahin cigaban ƙididdigar tattalin arziki na bayyana cikin faɗin kasar.

Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Archbishop Daniel Okoh ya fitar yayin jawabin taya Najeriya murnar cika shekaru 65, ya kuma bukaci shuwagabanni da su samar da abinci, tsaro, kare rayukan al’umma da samarwa da matasa ayyukan yi.

Ya kuma kara da cewa tabbataccan haɗin kai shine jigon cigaban kowacce al’umma tare da samar da wadataccan abinci, da kuma tsaro a kowanne yanki

.
Sun kuma yadda Najeriya na da mashahurin kundin cigaba ta bangaran ilimi, lafiya, masana’antu, noma da ma bangaran sadarwa tun kafin samun yancin kai.

Kazalika kuma ya yi addu’a ga shuwagabannin ƙasar da su ƙara himmar karfafa gwiwa wajen ganin an sake gina sabuwar Najeriya mai cike da tsaro.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci jam’ian tsaro da su haɗa kai da al’umma wajen ganin an samu tabbatar da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: