Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce jami’an soji sun samu nasarar kama ‘yan ta’adda akalla 450, da sauran masu aikata laifuka a fadin kasar nan a cikin watan Satumban da ya gabata.

Daraktan yada labarai na tsaro Manjo Janar Markus Kangye ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
Ya ce ‘yan ta’adda 39 ne suka mika wuya, yayin da aka ceto mutane 180 a yayin sumamen.

Ya kuma ce an kwato makamai 63, harsasai 4,475 da kuma wasu kayayyaki 294 da suka hada da gurneti, da kayan fashewa, da rediyon hannu, babura da motoci.

Ya kara da cewa dakarun Operation Delta Safe sun dakile satar mai da kudinsa ya kai Naira 112,175,220, wanda ya kunshi lita 49,321 na danyen mai, da lita 6,970 na gas na mota, sai lita 1,900 na kananzir, da kuma lita 1,475 na man fetur.
A cewarsa sojojin sun kuma kama bindigu masu sarrafa kansu, gurneti, bindigu na gida, harsasai masu rai da wasu harsasan kala daban-daban da sauran kayyakin aikinata ta’addancinsu.
Sannan a bayyana cewa rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Gabas Operation HADIN KAI, ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a tsakanin ranakun 23 zuwa 30 ga watan Satumban, akan ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.
Ya ce sojojin kasa tare da hadin gwiwar na sama, da jami’an hadin gwiwa na tsaro da kungiyoyin tsaro na cikin gida, sun gudanar da ayyuka a kananan hukumomin Konduga, Gwoza, Mafa, Gukba, Monguno, Damboa, Biu da Kukawa na jihar Borno.
Sai Kananan hukumomin Madagali, Hong da Mubi ta kudu na jihar Adamawa, sai kuma karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe.
A cewarsa, ayyukan sun yi sanadin mutuwar ‘yan ta’adda da dama, da kwato makamai, da lalata sansanoninsu, da kuma tarwatsa hanyoyin sadarwa.
Kazalika ya ce kokarin ya kuma tallafawa sake tsugunar da ‘yan gudun hijira da ayyukan noma a yankin.