Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Abia sun ce sun yi nasarar ceto jarirai takwas da kananan yara goma da aka sace bayan wani samame da suka kai kan wata kungiyar safarar yara a garin Aba da kewaye.

Rundunar ta kuma kai ga kama wasu mutane goma da ake zargi da hada baki da kuma satar yara.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Maureen Chinaka ya fitar, ya ce sun kaddamar da aikin ne biyo bayan wani korafi da suka samu a ranar 27 ga watan Satumba 2025.

Sanarwar ta ce a ranar 27 ga watan na Satumba da misalin karfe 09:40 na safe ne suka samu rahoto cewa wata mata ‘yar Abakaliki ta jihar Ebonyi ta zo garin Aba da ‘ya’yanta guda biyu mace da namiji da wani matashi ya yi lalata da ita, ya tsere da mata da ƴaƴan.

Sai dai ya ce bayan samun bayanan sirri a ranar 8 ga watan Oktoban nan, jami’an rudunar suka kai sumame gidan da ake zargin ana tsare da yaran da aka sace, inda suka kama mutane biyar da ake zargin.
Kazalika ya ce a ci gaba da binciken a ranar 9 oktoban, jami’an sun sake kai sumame wani gidan da ake boye yara da ke kan titin Aba zuwa Owerri, inda aka gano wasu yaran da aka sace, sannan suka kama mutane hudu da ake zargi, tare da ceto jarirai bakwai da yara uku.
Har ila yau ya ce a jiya Juma’a jami’an ‘yan sanda sun kama wani da ake zargi, Brittney Oyemuwa, tare da kubtar da wani yaro guda a hannunsa, kuma ana ci gaba da bincike a sashin binciken manyan laifuka na jihar.
A halin yanzu dai dukkan wadanda ake zargin na tsare, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike a hukumar binciken manyan laifuka ta jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Danladi Isa, ya tabbatar da kudurin rundunar na magance miyagun laifuka da kuma tabbatar da tsaron dukkan mazauna Jihar, tare da bukatar jama’a da su kasance masu sanya ido, da kula ‘ya’yansu yadda ya kamata.