Rundunar ‘yan sanda a Ebonyi ta tsare wani mutum Chukwuma Onwe, bisa zargin sayar da dansa mai kwanaki biyar da haihuwa akan Naira miliyan 1.5.

Onwe wanda dan asalin karamar hukumar Izzi ne a jihar, an kama shi ne a lokacin da matarsa mai suna Philomena Iroko ta sanar da makwabciyarta, inda ta sanar da ‘yan sanda matakin da mijin ya dauka.
Rahotanni sun ce an sayar da jaririn ne ga wata mata mai suna Chinyere Ugochukwu, wadda itama tuni ‘yan sanda suka kama mata.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Jihar Joshua Ukandu ne ya tabbatar da hakan a ranar Asabar a Abakaliki, inda ya ce an kwato jaririn daga hannun wanda ake zargin ta saya.

Kakakin ya ce an kama mahaifin yaron ne tare da wadda ake zargi da saye a ranar Juma’a a unguwar Azugwu da ke karamar hukumar Abakaliki a jihar.
Ya ce mahaifiyar yaron ta shaida musu cewa mijin nata ya dauke ɗan ne ba tare da saninta ba, inda daga baya ya ce ya kai’wa ƴar uwarsa domin ƙarin samun kulawa.
Kakakin ya ce za su fara gudanar da bincike akai.