Shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP kuma gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed, ya soki wasu ‘ya’yan jam’iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, inda ya bayyana matakin da suka dauka a matsayin abin kunya.

Shugaban ya kuma ce babu gudu babu ja da baya, a babban taron jam’iyyar PDP na kasa da za a yi a garin Ibadan na jihar Oyo tsakanin ranakun 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba.

Da yake jawabi yayin kaddamar da karamin kwamitin yada labarai da sadarwa na jam’iyyar na kasa a ranar Asabar a Abuja, gwamnan ya jaddada aniyar jam’iyyar na ci gaba da gudanar da shirye-shiryen babban taron kamar yadda aka tsara, inda ya jaddada cewa jam’iyyar PDP za ta ci gaba da kasancewa a dunkule, da juriya, da kuma kudurin fitowa da karfi gabanin kakar zaben 2027.

Jam’iyyar PDP dai ta fada cikin rikici ne tun bayan gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa a zaben 2023, wanda ya haifar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da ministan babban birnin tarayya na a yanzu Nyesom Wike.

Rikicin jam’iyyar dai ya biyo bayan ficewar wasu gwamnoni da suka hada da na jihar Delta Gwamna Sheriff Oborevwori da na Akwa-Ibom Umo Eno.

Yayin da a ranar Talata ne gwamnan jihar Enugu Peter Mbah, zai bayyana jam’iyyar APC a matsayin jam’iyyar da zai koma, inda wasu ke hasashen cewa gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri shima ka iya biye masa baya.

Sai dai gwamna Bala ya bukaci shugabannin jam’iyyar da su kara zage damtse wajen sake fasalinta, inda ya jaddada cewa ‘ya’yan jam’iyyar da ‘yan Najeriya baki daya na fama da wahalalu.

Ya kuma bayyana amincewarsa ga mambobin kwamitin yada labarai da sauran masu ruwa da tsaki, inda ya bayyana amincewa da babban taron da ke tafe da kuma karfin jam’iyyar PDP, yana mai cewa jam’iyyar PDP ce za ta yi nasara a zaben na 2027 mai zuwa a ƙASAR.

Leave a Reply

%d bloggers like this: