Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar birnin Tarayya Abuja a yau Lahadi, zuwa Rome babban birnin kasar Italiya, domin halartar taron shugabannin kasashen Aqaba da na matakin gwamnati.

Mai bai’wa shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, ya ce taron da shugaban zai halarta zai mayar da hankali ne musamman kan matsalar tsaro, a Afirka ta yamma, inda za a fara a ranar Talata 14 ga watan Oktoba.

Sanarwar ta ce, taron zai hada shugabannin kasashe da gwamnatoci, manyan jami’an leken asiri da sojoji na kasashen Afirka da wakilan kungiyoyi masu zaman kansu da na gwamnati, domin tattauna matsalolin tsaro a yankin na Afirka.

Taron wanda Sarki Abdullah na ll na kasar Jordan ya kaddamar a shekarar 2015 kuma Masarautar Hashemite ta kasar Jordan da gwamnatin kasar Italiya suka jagoranta, taron tsarin na Aqaba wani shiri ne na yaki da ta’addanci da ke fahimtar kalubalen tsaro da suka shafi yammacin Afirka.

A yayin taron, mahalarta taron za su yi musayar ra’ayi kan yanayin tsaro, da ake ciki a yanzu a Afirka ta Yamma, tare da karfafa hadin gwiwa tsakanin abokan huldar yankin da na kasa da kasa don tunkarar kalubalen tsaron kan iyaka, tare da samar da dabarun dakile barazanar ta’addanci a kasa da ruwa.

Bayo ya ce shugaba Tinubu zai tattauna da sauran shugabannin kasashen, domin lalubo hanyoyin dakile matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin.

Shugaban zai samu rakiyar karamar ministar harkokin wajen Najeriyar Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, ministan tsaro Mohammed Badaru Abubakar da mai bai’wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, da darakta janar na hukumar leken asiri ta kasa NIA Ambasada Mohammed Mohammed da kuma sauran manyan jami’an gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: