Kungiyar SERAP mai rajin kare tattalin arzikin Najeriya ta yi kira ga sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC Farfesa Joash Amupitan da ya nuna jajircewa wajen kawo karshen rashin hukunta masu aikata laifukan zabe a Najeriya.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, mai dauke da sa hannun mai magana da yawunta, Kolawole Oluwadare ya fitar, SERAP ta bukaci Amupitan da ya tabbatar da cewa INEC a karkashin shugabancinsa ba za ta amince da dukkan wasu ayyukan laifi na zabe ba.

SERAP ta yi gargadin cewa magance matsalar, da rashin hukunta masu aikata laifukan zai karawa ‘yan siyasa kwarin gwiwar ci gaba da zagon kasa ga dimokradiyyar Najeriya.

Acewarta rashin hukunta laifukan da aka yi a baya shi ne babban abinda ya kawo cikas ga gudanar da sahihin zabe a Najeriya. inda ta ce ya zama wajibi sabon shugaban ya nuna cewa INEC a karkashinsa ba za ta amince da laifukan zabe a zaben kasar ba.

Kungiyar ta ce a yayin zaben 2015 an samu aikata manyan laifukan zaɓe da suka hadar da tashe-tashen hankula, cin hanci da rashawa, siyan kuri’u, da dai sauransu.

Kungiyar ta kuma ta jaddada cewa ba za a iya gudanar da sahihin zabe ba, ba tare da tantancewa da kuma yin adalci kan laifukan zabe ba.

A ranar Alhamis ne dai shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sanarwa da naɗin Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar, bayan kammala wa’adin tsohon shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: