Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama wani dan kasuwa mai shekaru 52, Ejiofor Godwin Emeka a filin sauka da tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano da ke Jihar Kano dauke da miyagun kwayoyi.

Mai magana da yawun hukumar na Ƙasa Femi Babafemi ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa.
Ya ce an gano jimillar hodar ibilis 127 da ya boye a cikin al’aurarsa da cikinsa bayan kwanaki da aka kwashe ana fitar da su.
Femi ya ce mutumin wanda ke gudanar da harkokin shagunansa a Legas da Onitsha a jihar Anambra, inda hukumar ta tsare shi a hannun hukumar ta bayan isowarsa daga kasar Thailand ta jirgin Ethiopian Airlines a ranar Laraba 8 ga Oktoban nan, bisa samun sahihan bayanan sirri.

Ya ce da fari sun gano hodar iblis 58 a cikin wandonsa, inda kuma a lokacin da aka fara bincikar lafiyarsa aka sake gano 69, inda adadinsu ya kai ya kai 127, mai nauyin kilogiram 1.388.
