Hukumar kare haƙƙin ɗan’adam ta ƙasa reshen jihar Kano ta ce ta karɓi ƙorafe ƙorafe da a ke zargi kan cin zarafin ɗan’adam da yakai 172 a watan Satumba.

Mai sanya ido a hukumar Alhaji Shehu Abdullahi ne ya bayyana hakan cikin tattaunawa da kamfanin dillanci labarai na ƙasa NAN a Kano yau Litinin.


Ya ce a yanzu sun yi nasarar magance ƙorafe ƙorafe 122 yayin da sauran 50 su ke aiki a kansu.
Ya kuma ƙara da cewa ƙorafe ƙorafe 130 waɗanda su ka shafi mata da kuma ƙananan yara ne.
Sannan akwai ƙorafe ƙorafe a kan ma’aurata, yara da kuma gaza ɗaukar nauyin iyali da matsalar da ta shafi harkokin cikin gida.
Daga ƙarshe ya ja hankalin ma’aurata da su zama masu haƙuri da juriya wajen sauke dukkan haƙƙin da ya rayata a kansu.