Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama Jeriel Peter mai shekaru 71, bisa zargin kashe matarsa Miltha Jeriel mai shekaru 67 a karamar hukumar Demsa da ke jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Suleiman Nguroje ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Yola.

Ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 6 ga watan Nuwamba, bayan lamarin da ya faru a ranar 4 ga watan Nuwamba, biyo bayan wata rashin fahimta da ta faru a wani dakin shan giya tsakanin ma’auratan.

A yayin rikicin rahotonni sun wanda ake zargin ya farwa matar ta shi ne, ta hanyar caka mata wuka da gatari a jikinta.

Ya ce bayan samun rohoton rundunar ta tura jami’an ‘yan sanda karkashin jagorancin jami’in ‘yan sanda baturen ƴan sandan yankin Dibishin Demsa zuwa wajen da lamarin ya faru.

Sanarwar ta kara da cewa,Nan take aka garzaya da wanda aka hallaka zuwa Asibiti inda aka tabbatar da mutuwarta.

Nguroje ya ce an ajiye gawarwakinta a dakin ajiyar gawa na asibiti domin yin bincike.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar CP Dankombo Morris, ya yi Allah-wadai da aika-aikar, ya kuma umurci sashin binciken manyan laifuffuka na Jihar da ya dauki fara binciken lamarin tare da tabbatar da bincike na gaskiya.

Morris ya yi gargadi game da duk wani tashin hankali na cikin gida kuma ya bukaci jama’a da su nemi warware rikici cikin lumana.

Ya kuma kara tabbatarwa mazauna garin cewa rundunar ta ci gaba da jajircewa wajen ganin an yi adalci kuma babu wani mai laifi da ya tsira daga hukuncin da ya dace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: