Aƙalla ƴan bindiga sama da 200 ne suka shiga ƙauyukan Sabon Gida, Sararai, Kurebe da Rafin Kanya yayin da suka kashe mutane 21 sannan suka yi garkuwa da mutane 40.

Ƙauyukan na ƙarƙashin ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Nijer.

An kai harin ne a jiya Litinin yayin da ƴan bindigan suka je garin a kan Babura ɗauke da muggan makamai.

Wani da al’amarin ya faru a gabansa ya shaida cewar, ƴan bindigan sun shiga gida-gida tare da kashe mutane sannan su tafi da wasu.

Baya ga mutanen da aka kashe akwai wasu da suka samu raunuka kuma suna karɓar magani.

Mun tuntuɓi kakakin hukumar ƴan sandan jihar Naija Wasiu Abiodun  ko suna da masaniya a kai, sai dai har lokacin da muke kammala wannan rahoto ba samu damar ɗaga kiranmu ba.

Harin na zuwa ne ƙasa da mako guda da naɗa sabbin hafsoshin tsaro a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: