Bayan sauyin wurin aiki da aka yiwa tsohon kakakin ƴan sanda na jihar Kano SP Magaji Musa Majia.

Rundunar yansandan Jihar Kano a yau Alhamis 24/01/2019 ta na’da Abdullahi Haruna dan asalin Jihar Jigawa daga karamar hukumar Kiyawa, a matsayin sabon kakakin rundunar wanda ya maye gurbin SP Magaji Musa Majia amnipr da aka yiwa canjin wajen aiki zuwa Jihar Yobe.

Rundunar ƴan sandan ta ƙasa dai ta sauyawa Majia wurin aiki ne a ranar talata inda aka umarceshi da ya koma sabon wajen aikin nasa ba tare da ɓata  lokaci ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: