Jam iyyar APC mai mulki ta samu nasara a ƙaramar hukumar Dala inda ta samu ƙuri u 2,905 yayin da jam iyyar PDP ta samu ƙuri u 3,138.

A cewar baturen zaɓen, ba a samu tashin hankali a ƙaramar hukumar Dala ba.
Sai dai wakilin jam iyyar PDP a zauren tattara sakamako Aliyu Sani Madaki ya yi ƙorafi an samu rikici a ƙaramar hukumar.

Ya ce har kwamishinan ƴan sanda ya halarci ƙaramar hukumar Dalan inda ya ganewa idonsa yadda aka samu hayaniya a yankin.
