A cigaba da karɓar sakamakon zaɓen gwamna wanda ka ƙarasa Jam iyyar APC ta samu nasara a zaɓen Gama inda ta samu ƙuri u 10,536 yayin da jam iyyar PDP ta samu ƙuri u 3,409.

Sai dai bayan bayyana sakamakon ne wakilan jam iyyarPDP suka fice daga ɗakin tattara akamakon, yayin zantawarmu da Shugaban riƙo na jam iyyar PDP Rabi u Sulaiman Bichi ya ce babu buƙatar su zauna domin sakamakon da aka kawo ba dai dai bane.

Jam iyyar PDP dai ta zargi jam iyyar APC da kawo wasu mutane daban wanda suka yi zaɓe  a gaman,inda aka samu tashinhankali, al amarin da ƴan jam iyyar APC suka musanta lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: