Gwamnatin APC ta shugaba Buhari a Najeriya ta yi iƙirarin cewa ta samar da guraben ayyukan yi sama da miliyan 12 a tsakanin wa’adin mulkinta na farko.

Ministan watsa labarai Alhaji Lai Mohammed ya shaida wa BBC cewa sabbin guraben ayyukan sama da miliyan 12 sun kunshi wadanda suka samar kai-tsaye da kuma wadanda suka taimaka aka samar.
Ya ce sun samar da sabbin ayukkan ne a fannin noman shinkafa da kuma shirin ciyar da dalibai a makaranta wanda ya samar da aikin yi ga masu dafa abinci.

Sannan ya ce N-Power ya samar wa matasa dubu biyar aikin yi da kuma shirin bayar da tallafi ga kananan ‘yan kasuwa na tireda moni wanda ya samar da sabbin ayyukan yi ga mutane sama da miliyan biyu.

Matsalar rashin ayyukan yi na cikin matsalolin da ke addabar ‘yan Najeriya.
Kiyasi ya sha nuna cewa miliyoyin matasa majiya karfi ne ke zaman kashe wando a kasar, a yayin da wasu karin miliyoyin ke kammala manyan makarantu duk shekara ba tare da samun ayyukan yi ba.
Wasu na ganin ikirarin gwamnatin na samar da ayyukan yi ta hanyar ba mutane tallafi ba zai zama hujjar samar masu da aikin da za su ci gaba da dogaro da shi ba.
Wani rahoto na baya-bayan nan da hukumar kiddidiga a Najeriya ta wallafa ya nuna cewa yawan marasa aiki a kasar ya karu da kusan kashi 23 cikin 100.
Hakan na nuna cewa ‘yan Najeriya marasa aikin yi sun kai Miliyan 20.
Amma Ministan ya ce sun samu alkalumman na ayyukan da suka samar ne a bangaren noma daga kungiyar manoman shinkafa ta kasa.
“Sabbin ayyukan da muka samar sun yi tasiri sosai ga bunkasar tattalin arziki,” in ji shi.
BBC Hausa.