LEMON KOKOMBA DA KARAS

Tare da maryam Muhammad Ibrahim

Uwargida da amarya barka da war haka sanumu da ƙara haduwa ta cikin mujallar Matashiya

Kayan haɗin sune Kamar haka
Karas
Kokomba
ɗanyar citta
Maisa kamshin lemon sukari
Da farko zaki Samu kokomba da karas ki kankare bayan karas ɗin, sai ki yanka shi kanana shi ma kokomba ki wanke shi ki yanka shi Kamar yadda kika yanka karas, sai ki dakko ɗanyar cita ki kankare bayan a dafa citar kaɗan ake sawa sai ki haɗesu dukka, ki markaɗa a bilanda sai ki ƙara ruwa daidai yadda zai isheki, sai ki tace sai ki sa sukari da kuma Maisa kamshin lemo ki juyashi ya juyu asa kankara ko kisa shi a firji wannan lemon yanada matukar ammafani a jikin ɗan adam da fatan za a gwada.