Hukumar kula da jarrabawar shiga jami a ta bayyana cewa za a sake jarrabawar daga 20 ga watan da muke ciki ga wuraren da aka gaza tantance adadin ɗaliban da suka zana jarrabawa.

Shugaban Faresa Ishaq Oloyede ya ce hakan ya faru ne sanadin kutse da aka yi cikin shafin nata tare da ƙara maki ga wasu mutane da kuma mutane waɗanda basu bi ƙa idar gudanar da jarrabawar ba

Ciki wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban hukumar ta ƙasa sun kasance masu bawa mutane haƙuri bisa yadda lamarin ya kasance.

Mujallar Matashiya ta gano cewa wannan shi ne karo na uku da hukumar ke ayyana ranar da za ta saki sakamako.

Leave a Reply

%d bloggers like this: