Yau makwanni uku kenan cif cif da yin awon gaba da magajin garin Daura wanda aka yi itifaƙin cewa masu garkuwa da mutane ne suka sace shi sai dai har yanzu babu labarin matsayin da yake.

Har yanzu dai gwamnatin ta gaza ceto rayuwarsa duk da kasancewarsa sirikin dogarin shugaba Buhari kuma magajin garin Mahaifar shugaban ƙasa.
A dai dai lokacin da mahara ke ci gaba da kai hare hare da sace mutane a tsakanin jihohin Zamfara da Katsina.

Sai dai wasu mazauna ƙaramar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara sun musanta iƙirarin gwamnatin tarayya na tarwatsa ƴan tada ƙayar baya a wata zantawa da suka yi da mujallar Matashiya

Ko da yake a yau ma gwamnan jihar Katsina ya tashi jirgi sukutum don zuwa Abuja tare da tattauna da shugaban ƙasa a kan matsalar tsaro da ta addabi jihar.