A cigaba da tantance sunayen Wanda Shugaba Muhammad Buhari ya aike majalisar dattawa a matsayin Wanda zai nada Ministocin.
Yanzu haka tun mislain karfe 12:30 na rana aka soma tantace wasu daga cikin su.
A yau Alhamis an tantance Tayo Alasoadura daga jihar Ondo Kuma ya kasance tsohon Sanata ne tun a shekarar 2015/2019.
Sai Kuma Mustapha Shehuri daga jihar Borno Wanda a baya shine karamin minista na ma’aikatar ayyuka, gidaje da lantark.

Haka zalika an tantance Gen Bashir Magashi daga jihar Kano inda ya amsa tambayoyi game da matsalolin harkar tsaro anan majalisa ta gamsu da irin amsoshin da bata.
Sai Kuma Abubakar Aliyu daga jihar Yobe ya kasance tsohon mataimakin gwamnnan jihar Yobe a shekarar 2009/2019.

Yanzu Wanda suke a layi da za’a tantancesu a yau sune Niyi Adeboye daga jihar Ekiti, sai Timpire Silva Daga Bayelsa.
Akwai Kuma Ramatu Tijjani da ta fito daga jihar Kogi.
Sai Muhammad Abdullahi Daga Nasarrawa.
Da Sunday Dore daga Jihar Oyo.

Leave a Reply

%d bloggers like this: