Assalamu alaikum mai girma gwamna da fatan kana cikin ƙoshin lafiya, Allah ya ƙara shiga cikin lamuranka na shugabanci na yadda za a kyautatawa al ummar da ake mulka.
Bayan gaisuwa mai yawa zan yi amfani da wannan dama don yabawa da namijin ƙoƙarinka bisa ɗaukar mutane matasa waɗanda za a kaisu ƙasar waje don ƙarin ilimin sana o i daban daban, tabbas wannan nasara ce musamman ma idan aka ce ilimin sana ar da za su ƙaro ba mu da masu yi a jiyar kano.
Mai girma gwamna kamar yadda kake da shekaru na girma tare da hankali da kaifin basira na yadda za a kawo hanyoyi na cigaba a jihar da kake jagoranta, ina mai farin cikin sanar da kai cewa akwai matasa da yawa a jihar Kano da suke da ƙoƙarin horas da mutane sana o i don su tsaya da ƙafarsu.
Kamar yadda Allah ya albarkaci wannan jiha da matasa masu basira da suka iya sana o i kuma hakan zai bunƙasa tattalin arziƙin jihar Kano.
Mai girma gwamna zan bada misali, ni kaina ko kamfanin da nake jagoranta, muna horas da matasa sana o i daban daban kyauta a bisa cigaban da muke samu na yau da kullum duk da dai babu wani tallafi ko yabo da ya taɓa fitowa a gwamnatance.
Mai girma gwamna ko iya ƙoƙarin samar da gidan jarida na Hausa da ya shahara a duniya aka kalla mujallar Matashiya ta cancanci dukkan wani tallafi daga gwamnati, mutanem da ke aiki a wannan gidan jarida ƴan jihar Kano ne, kamfanin a jihar Kano yake, kafin kowa ya amfana da wannan kamfani sai ƴan jihar Kano sun amfana, amma daidai da biro ba a taɓa bamu a gwamnatance ba, ko wajen zama namu na kanmu bamu da shi duk da gudunmawar da muke bawa al ummar gwamnati.
A ƙalla mun horas da matasa fiye da mutum 500 ƴan asalin jihar Kano kuma ma tabbata ko kai ka ɗauki nauyinsu a matsayinka na gwamna dole a jinjina maka don ka yi namijin ƙoƙari.
Da yawan mutane sun san haka kuma wasu ma kana da kusanci da su na san idan ka bincika za ka tabbatar da hakan.
Mai girma gwamna iya ƙoƙarin da muka iya bai wuce na mu koyar da sana ar ba amma matasan da muka koyar haka muke barinsu babu wani tallafi da za su yi jari ko cigaba da dogaro da kansu.
Akwai ire irenmu a jihar nan mai albarka wasu an sansu wasu ba a sansu ba, mai girma gwamna me zai hana a ƙarfafawa na gida gwiwa tare da basu tallafi tunda ƴan jihar Kano ne kuma mutanen da ke amfana ma ƴan asalin jihar ne?
Na tabbata ƙara ƙarfin gwiwar zai sa su ƙara ƙaimi don ganin an zaburar da wasu masu ƙoƙari ko tunanin farawa, hakan zai taimaka matuƙa ko da a fannin tsaro tunda binciken masana ya nuna cewa matasan da ke amfkawa halin ashsha suna yi ne sanadin rashin sana ar da za su yi.
Idan har akwai wani kaso da za a samu a kai waje don amfanar matasa al hali masu yin ƙoƙarinsu basa samun tallafi, tabbas za a yi tufka ta baya na warwarewa, za a sanyayar mana da gwiwa, za a sa mu karaya da abinda muke yi tunda dai gwamnatin muke wahaltawa.
Mai girma ina ina fata za ka yi amfani tare da duba da idon basira a bisa abinda nake nufi kasancewarka Dakta a Karatu.
Allah ya taimaki shugabancinka
Allah ya taimaki jihar Kano
Allah ya taimaki al ummar jihar Kano
Allah ya taimaki Al ummar Najeriya baki ɗaya.
Abubakar Murtala Ibrahim
26/07/2019
23/11/1440


