Ministocin da shugaban ƙasa Muhammadu Buhariya aike majila don tantancewa zna sa rai za a rantsar da su a ranar 21 ga watan agustan da muke ciki.

Fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwar cewa a yau talata, ta ce misitocin da aka tantance za a rantsar da su a ranar 21 ga watan nan.
da yawa daga cikin ministoci 43 da shugaba Buhari ya aike da sunayensu, tsofaffin ministocinsa ne a zangon mulkinsa na farko.

Hakan ne ma ya sa wasu daga cikin yan Najeriya ke tunanin cewa ba za ta sauya zani ba ganin cewa akwaimutanen da a baya ya basu muƙaman kuma ba su taɓuka abin arziƙiba.
