Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta cafke Shugaban Gidan Talabijin na jihar Kwara bisa zargin sama da fadi da yayi da Wasu filaye har goma.

Shugaban Gidan Talabijin din Mai suna Abdulfatai Adebowale, an kamashi ne tare da Wasu Ma’aikatan sa guda biyu.
EFCC dai na zargin su ne dai da juya akalar filaye goma mallakin Gidan Talabijin din zuwa Mallakinsu Wanda suka siyar don biyan bikatunsu.

Wasu Ma’aikatan gidan Talabijin din ne suka mika kokensu ga hukumar ta EFCC tun a shekarar 2014 Inda suka bayyana cewa Adebowale ya siyar da filaye mallakin Gidan Talabijin na jihar Kwara.

EFCC yanzu haka suna gudanar da Bincike akansu.