Rundunar yansandan jihar Legas tayi tayi nasarar kubutar da wasu yan Mata 19 dake dauke da juna biyu, da kuma wasu kananan yara guda 4 Wanda Rundunar ke zargin sato su akayi.

Mai magana da yawun Rundunar yansandan jihar Legas Dsp Bala El-kana shine ya tabbatar da hakan inda yace an kama wasu Mata guda biyu Happiness Ukoma da Sherifat dukkaninsu yan kimanin shekaru 40 ne inda ake zarginsu da yin safarar mata da kananan yara.

Dsp El-kana yace an sato matan ne zuwa jihar legas inda ake musu ciki daga bisani a siyar da jariran akan naira Dubu dari uku zuwa biyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: