Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar litinin a matsayin Ranar hutu ga Ma’aikata don murnar Maulidin haihuwar Manzon Allah SAW.

Ministan Ma’aikatar cikin Rauf Aregbedola shine ya bayyana hakan ta cikin kunshin sako Kakakin Ma’aikatar Muhammad Manga ya fitar inda aka rabawa manema labarai a yau.

Aregbesola yace an ware ranar ne ya zama hutu don tunawa da ranar zagayowar haihuwa fiyayyen halita.

Ya kara da cewa Al’ummar Najeriya suyi amfani da ranar don yiwa kasa addu’ion samun zaman lafiya da Habbakar Tattalin Arziki a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: