Kungiyar SERAP da wasu kungiyoyi a najeriya sun shigar da Kara gaban babban kotun Tarayya dake Abuja.

Inda suke Kira ga kotun da ta dakatar da Shugaban kasa Muhammmad Buhari da Ministan Kudi Kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmad akan Shirin su na na fitar da naira Biliyan 37 don gyaran Majalisun kasar nan Biyu.
Haka zalika Kungiyoyin sun bukaci Kotun da ta hana Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawal da Takwaransa na Majalisar wakilai Femi Gbajabiamila daga karbar wadannan kudade, da sunan gyaran majalisa.

A cewar su har sai Al’umma ta gamsu da cewa yin gyaran Majalisun abu ne mai Muhimmaci.

Haka zalika sun Kuma bayyana cewa a yanzu akwai matsalolin da Ya kamata Shugaban kasa Muhammmad Buhari ya sa a gaba ba wai gyaran Majalisun biyu ba.