A daidai lokacin da ake zargin gazawar shugabanni a fanjin tsaro, fadar shugaban ƙasar Najeriya ta zargi masu riƙe da sarautar gargajiya da hannu cikin harin ƴan bindiga a Katsina.

Sanarwar da babban mataimakin shugaban ƙasa kan kafafen yaɗa labarai Mallam Garba Shehu ya fitar ya ce akwai sa hannunsu shi yasa lamarin ya ƙi ƙarewa.
Yayin tattaunarwa da aka yi da shi a Channel TV ya ce masu riƙe da sarautar gargajiya ke ɗaukar nauyin ƴan bindigar.

Ya ƙara da cewa akwai wasu sarakuna da aka samu da hannu a cikin lamarin yayin da ake gudanar da bincike a jihar Zamfara.
