Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana Najeriya cikin jerin kasashen da ba sa dauke da cutar polio, tun bayan kwashe shekaru ana yaki da cutar a Kasar.

Ofishin Hukumar dake Congo Brazzaville ce ta sanar da hakan inda tace saboda rawar da hukumomin lafiya da kungiyoyin agaji da jami’an kula da lafiya suka taka wajen ayyukan rigakafi da wayar da kan jama’a wajen karbar maganin, yayi tasiri wurin yaki da cutar.

Haka zalika Hukumar ta Lafiya ta bayyana Najeriya a matsayin mai Kasa mai dimbin tarihi wajen kula da lafiyar jama’a a Najeriya da Afirka da kuma duniya ta fannin yaki da cutar polio wadda ta nakasa yara da dama.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana wannan nasara a matsayin gagarumar cigaba ga al’ummar kasar wanda ya nuna jajircewa wajen harkar kula da lafiyar al’umma.

Madogara Rfi

Leave a Reply

%d bloggers like this: