Gwamnatin Najeriya ta yi Allah wadai da matakin rushe gine-ginen Difilomasiyyarta 2 da ke birnin Accra na kasar Ghana,

tare da neman karin bayani daga gwamnatin kasar game da musabbin hakan.

Ministan harkokin wajen Najeriyar Geoffrey Onyeama shine ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter jim kadan bayan bayyanar batun rushe ginin Diflomasiyyar.
,
Inda ya ce wajibi ne Ghana ta dauki matakin kare lafiyar ‘yan Najeriya da ke cikin kasar.

A cewar Onyeama tuni gwamnatocin kasashen biyu suka fara tattaunawa kan batun wanda bayanai ke cewa anyi amfani da motar rusau wajen rushe gine-ginen Diflomasiyyar Najeriyar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa tuni al’ummar kasar ta Ghana suka fara farmakar ‘yan Najeriyar da ke cikin gine-ginen tare da kwashe kayayyakinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: