Majalisar ɗinkin duniya ce ta ware dukkanin ranar 23 ga watan Yunin kowacce shekara a matsayin ranar tunawa da zawarawa a duniya.

An ware wannan rana ne don tallafawa zawarawa da suke a ƙasashe daban daban tare da duba irin ƙalubalen da suke fuskanta a cikin rayuwarsu.
A kan yi bikin a ƙasashe daban daban don duba halin da suke ciki tare da samar da hanyar da zata inganta rayuwarsu.

A wannan shekara ta 2020 an maida hankali ne wajen wayar da kan zawarawan kan ƴancinsu da sauran al amuran rayuwa.

Rajinda Paul Loomba ne ya samar da wata ƙungiya don wayar da kan zawarawa, a sakamakon mahaifiyarsa da ta shiga zawarci tana shekara 37.
An ƙaddamar da gangamin wayar da kan zawarawa a ranar 26 ga watan mayu na shekarar 2005 a birnin landan.